A lokacin da Obama ke ganawa da shugaban Turkiyya a taron kolin manyan kasashe na G-20 yace “Zamu tabbatar da cewa duk wadanda ke da hannu sun fuskanci shari’a.”
Turkiyya dai ta tsaya kan bakarta na cewa shahararren malamin addinin Islaman nan ‘dan shekaru 75 da haihuwa Mallam Fethullah Gulen, ya na da hannu a juyin mulkin, wanda yanzu haka yake zaman hijira a jihar Pennsylvania ta Amurka, tun shekarar 1999. Sai dai Mallam Gulen, ya fito ya musanta alakarsa da juyin mulkin.
Turkiyya dai ta bukaci Amurka da ta mayar mata da Gulen, amma jami’an Amurka sunce har yanzu Turkiyyar ba ta basu wata shaidar da take nuna cewa Gulen na da alaka da yunkurin juyin mulkin da bai sami nasara ba, a kokarin hambare gwamnatin shugaba Erdogan. Amurka dai tace kafin yunkurin mayar da duk wani mutum wata ‘kasa dole ne sai an bayar da shaida kuma kotun Amurka ta amince.