Islam Karimov mai shekaru 78 a duniya ya kasance shugaba da ake mai kallon mai mulkin kama karya a kasar da ta ke tsakiyar Asia sama da shekaru 25.
Sanarwar gwamnatin na cewa, "al’ummar kasar nan, ina jin bakin cikin bayyana muku irin mawuyacin halin da shugabnmu ke ciki na rashin lafiya wanda ke kara tabarbarewa tun sa'oi 24 wanda a halin yanzu rai na hannun Allah.
Akwai wasu rahotanni da ke yawo cewa shugaban ya riga ya mutu, amma dai ba a tabbatar da mutuwarsa ba.
Kafar labarai ta Fergana ta fara ba da labarin makoki wanda za ayi a garin shugaba Karimov na Samarkand.
Ana zargin Karimov da yawan gallazawa 'yan adawa kuma bai nada wanda zai gaje shi ba.
Kungiyar rajin kare hakkin bil adama ta Huma Rights Watch ta ayyana Uzbekistan wacce take take 'yan cin bil adama.