Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiya Ta Musanta Kulla Yarjejeniyar Tsagaita Wuta da Mayakan Kurdawa


Turkey Erdogan, shugaban kasar Turkiya
Turkey Erdogan, shugaban kasar Turkiya

Cikin 'yan kwanakin nan gwamnatin Amurka ta sanar cewa Turkiya tayi yarjejeniyar tsagaita wuta da mayakan kurdawa dake yaki a kasar Siriya

Gwamnatin kasar Turkiyya ta musanta ikirarin da Amurka ta yi, na cewa wai ita Turkiyya din ta kulla wata yarjejeniyar tsagaita fada da mayakan Kurdawa, tace sam, ba zata daina fattatakar da take musu da jiragenta na sama ba a arewancin kasar Syria.

Amurka na son Turkiyya da ta daina kaiwa Kurdawan hare-hare ne, a maimakon haka ta maida hankalinta wajen yaki da kungiyar ISIS, to amma wani kakaki mai magana da sunan shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan yace maganar sulhun da Kurdawan “sam bata ma taso ba.”

Yace zasu ci gaba da fattakan Kurdawan har sai ranar da suka tashi daga inda suke, suka koma gabascin Kogin Euphrates.

XS
SM
MD
LG