Amurka tayi Allah wade da harin da aka kai a arewacin Kamaru, wanda ya kashe mutane akalla mutane 32, ya kuma jikkita fiye da wasu 80, da yanzu haka suke asibiti.
Jakadan Amurka, a jamhuriyar Kamaru, Michael Steven Hoza, ne ya furta haka a lokacin da ya kai ta’aziyar kasar Amurka, ga hukumomin kasar Kamaru, yace Amurka, na mika ta’aziya ga alumar kasar Kamaru, kuma ba zamu gaji ba wajen taimakawa kasar yakar ‘yan Boko Haram.
Jakada Hoza, ya ci gaba da cewa akwai yarjejeniya tsakanin Amurka, da Kamaru, domin bada labarai na siri yace yanzu haka zamu canja sabon salo domin taimakawa dakarun kasar ta Kamaru, da dabarun yaki domin gamawa da ‘yan ta;addan Boko Haram.
Kuma yace yana fata nan bada jimawa ba za’a ci galabar ‘yan ta’addan a fadain kasar Kamaru baki daya .
Your browser doesn’t support HTML5