Amurka da China Za Su Sake Ganawa Game da Yarjejeniyar Cinikayya Tsakaninsu

Shugaba Trump da Shugaba Shi (Xi)

Wasu masana ma na ganin cewar banbancin da ke tsakanin kasashen biyu ya yi girman da babu abin da zai hana su kara wa juna yawan haraji akan kayan da suke shigarwa kasashen junansu.

A farkon makon gobe ne za a koma birnin Washington DC a cigaba da tattaunawa akan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin China da Amurka, sai dai masu fashin baki sun ce akwai matsanancin banbancin ra’ayi kan batun a tsakanin bangarorin biyu tun bayan haduwarsu ta farko.

Kamar yadda takardun bukatar Amurka a wannan zama ke nunawa, tawagar wakilan shugaba Donald Trump ba wai kawai sun bukaci China ta kawar da gibin kasuwancin da ke tsakanin kasashen biyu na kimanin Dalar Amurka Biliyan $200 daga yanzu zuwa shekarar 2020 kadai ba ne, a’a har da bukatar zaftare harajin kayayyaki da kuma rangwamen gwamnatin kan manyan kayan kimiyya.

Ita kuma China so take Amurka ta daina tsoma baki ko nuna adawarta kan matsayin China a kungiyar yan kasuwa ta duniya, kuma ta bude kofar karbar kayayyakin kimiyyar China da kamfanonin gwamnatin Amurka ke son samu.