Kasar China ta kira barazanar da Shugaba Trump keyi na Karin kudin haraji akan kayayyakin da suke cinikayya da Amurka a matsayin wani yunkurin kai kasar makura da neman tozartawa,wanda kuma tuni ita ma tayi barazanar daukar matakin ramuwar gayya.
Kasar China dai ta mayar da martini ne a jiya lokacin da shugaba Trump yace yana shirin kara harajin dala biliyan 200 a kayan da kasar ta China take sayarwa Amurka musammam ma idan kasar taki ta sauya tabiu’nta.
Darektan hukumar kasuwanci na fadar White House,Peter Navarro ya shaida wa manema labarai a jiya Talata cewa, fadar ta White House ta baiwa kasar China damar da duk take bukata domin ta canza tabi’o’inta. Amma ta bi gaban kanta.