Amurka, Birtaniya Sun Ba Najeriya Shawara Kan Zaben 2019

A lokacin zanga-zangar rashin yarda da jinkirta zabe, Fabrairu 5, 2015.

Kasashen na Amurka da Birtaniya da kuma kungiyar ta tarayyar turai sun ce za su sa ido su ga yadda wannan zangon gangamin yakin neman zabe zai kasance.

Yayin da aka yaye lubalen gangamin yakin neman zabe a Najeriya, Amurka, Birtaniya da kungiyar tarayyar turai ta EU, sun yi kira ga hukumomin kasar da su kasance masu nuna dattaku wajen gudanar da zaben.

A wata wasika ta hadin gwiwa da bangarorin uku suka sanyawa hannu, sun nemi Najeriya da ta zama abin koyi ga sauran kasashe a nahiyar Afirka.

Kasashen na Amurka da Birtaniya da kuma kungiyar ta tarayyar turai sun ce za su sa ido kan yadda wannan zangon gangamin yakin neman zabe zai kasance.

A ranar Lahadin da ta gabata, hukumar zaben kasar ta INEC mai zaman kanta, ta ayyana cewa ta bude zangon fara yakin neman zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu da za a yi a ranar 16 ga watan Fabrairun badi.

Shin me ‘yan siyasa da masu kada kuri’a a kasar ke cewa dangane da wannan lamari? Saurari rahoton Babangida Jibril da ya aiko mana daga Legas:

Your browser doesn’t support HTML5

Amurka, Birtaniya Sun Ba Najeriya Shawara Kan Zaben 2019 - 3'15"