Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar CISLAC Ta Bude Cibiyar Kai Koken Cin Hanci Da Rashawa


Kungiyoyi Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Tir Da Matakan Gwamnati
Kungiyoyi Masu Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Sun Yi Tir Da Matakan Gwamnati

Wata kungiya mai zaman kanta ta dauki matakin marawa gwamnatin tarayya baya a yunkurin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta wajen bude ofishin kai kwarmato.

Kungiyar CISLAC mai sa ido a ayyukan yaki da cin hanci da rashawa ta bude wata cibiya mai suna ALAK da za ta taimaka wajen kulawa da masu kawo koke akan cin hanci da rashawa da kare yancin wadanda aka zargi da laifin cin hanci da ma wadanda aka tauye masu hakin su na dan Adam.

Shugaban Kungiyar CISLAC Auwal Musa Rafsanjani ya ce cibiyar za ta rika tattara bayanai tare da bin diddigin laifuka da suka shafi cin hanci da rashawa har a hukunta masu laifin baya ga taimakawa wajen shigar da koke koken.

Wanan Cibiya ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma an kafa ta ne tare da hadin gwiwa da Hukumomin Yaki da Cin Hanci da rashawa ta Kasa.

Bincike ya nuna cewa Najeriya na hasarar kashi ashirin da biyar cikin dari na arzikin ta a fanin cin hanci da rashawa kuma an shigar da kararraki da yawa amma har yanzu ba a hukunta kowa ba.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:

CISLAC ta bude ofishin kai koke-3:42"
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:30 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG