Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ake Fara Yakin Neman Zaben Najeriya Na 2019


Shugaba Buhari da Atiku a lokutan baya
Shugaba Buhari da Atiku a lokutan baya

Daga Yau Lahadi ne hukumar zaben Najeriya ta amince 'yan takar shugabancin Najeriya da 'yan takarar kujerun majalisar dattawa da ta wakilai su fara yakin neman zaben da za a yi a watan Fabrairun 2019.

A yau Lahadi 18 ga watan Nuwamba 2019, Hukumar zaben Najeriya ta dage takunkumi don fara kamfe din ‘yan takarar shugabancin Najeriya da na ‘yan majalisun dokokin tarayya.

Daraktan wayar da kan masu kada kuri’a na hukumar zaben INEC Osaze Uzzi ya bayyana haka a sanarwar da ya yi cewa hakan ya na cikin jadawalin zabe da tanadin dokar zabe ta 2010.

Za a gudanar da zaben na shugaban kasa da majalisun dokokin tarayya a ranar 16 ga watan Fabrairu na 2019, inda a ranar 2 ga watan Maris za a gudanar da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi.

Malaman addinai sun yi kira ga jama’a su bada gudumuwar su wajan tabbatar da zaman lafiya a daidai wannan lokaci mai muhimmanci a tarihin kasa nay akin neaman zabe da kuma gudanar da zabe.

Ga wakilinmu Nasiru Adamu El-Hikaya da cikkaken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG