Aminu Sule na 'Network For Justice' Ya Ce An Fi Tauye Hakki a Kasashen Bakar Fata

Tambarin Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban kungiyar Network For Justice ya danganta ranar kare hakkokin bil Adama ta duniya da abubuwan tarihin da Mandela ya yi
A bana ranar kare hakkokin bil Adama ta duniya ta zo daidai da ranar karrama marigayi Nelson Mandela wanda shi ma yayi gwagwarmayar kwatar 'yanci da kare hakkin jama'a da tabbatar da gaskiya da adalci. Albarkacin ranar ta yau ma'aikacin sashen Hausa a birnin Washington,DC Ibrahim Ka'almasih Garba ya tattauna da malam Aminu Sule shugaban kungiyar Network for Justice ta kare hakkokin bil Adama a Kaduna. Kafin Aminu Sule ya shiga bayani a kan kyawawan halayen marigayi Mandela, ya fara ne da yin matashiya game da ranar ta kare hakkokin bil Adama.

Your browser doesn’t support HTML5

Aminu Sule na Network for Justice a kan ranar 'yancin bil Adama da Mandela - 3:11