Dalili ke nan da ma wasu dalilai da kananan hukumomi suke neman a yiwa kundun tsarin mulkin kasar kwaskwarima. Gyaran zai basu 'yanci zasu kuma iya yin zabe lokacin da dokar ta tanada. Ban da haka gwamnoni ba zasu iya cigaba da rushesu ba
Shugaban ma'akatan kananan hukumomi a Najeriya ko NULGE, a takaice, Alhaji Ibrahim Kalil ya ce jan kafar da majalisun kasar ke yi kan gyara kundun tsarin mulkin kasar abun takaici ne. Ya nuna takaicinsa ne a taron kungiyar da suka yi a jihar Oyo domin zaban shugabannin kungiyar ta jihar. Ya ce gaskiya akwai takaici shi ya sa mutanen Najeriya ke shakkun mulkin kasar. Abun takaicin shi ne tun da majalisar wakilai ta yadda amma ta dattawa ki zaman samun daidaituwa tsakaninsu kamar yadda doka ta tanda ya cutura.
Kan batun yin nazari, Alhaji Kalil ya ce babu wani zarari da ya saura a yi domin an yi a duk fadin kasar. An tattara jawabai har ma da kasidu kan cancantar yin gyaran domin tabbatar da cikakkiyar dimokradiya. An kuma kashe makudan kudade domin kowa ya fadi albarkacin bakinsa. Abun da ya saura kawai majalisun su zauna su bi abun da mutanen kasar ke so su kuma aiwatar.
Kamata ya yi majalisun su fito su fadawa 'yan Najeriya dalilin da ya sa suka kasa aiwatar da gyaran. Dama ana zargin wata kila gwamnoninsu suka hanasu yin abun da ya kamata. Idan ba haka ba idan kuma ba rufa-rufa ko boye gaskiya ko son yin rashin da'a suke son su nuna ma duniya ba to su fito su yi abun da jama'a suke so. Kila suna son cin amanar mutanen Najeriya ne shi ya sa suna jan kafa a KAN al'amarin.
Ga Hassan Umar Tambuwal da karin bayani
.