Wasu mazauna Abuja sun ce in ba tare da an yi hukumci ba, wannan tashin hankalin zai kara yin muni.
A bayan zaben shekarar 2011, tashin hankali ya barke a Kaduna, inda aka kashe mutane fiye da 800. Mutanen Kaduna suka ce har yanzu wadanda suka aikata wadannan kashe-kashen su na yawonsu a kan tituna gabansu gadi.
Wani dan siyasa kuma mazaunin Kaduna, Sunday Mudakai,yace abin tayar da hankali ne, abin bata rai ne, kuma abin firgitarwa ka ga mutumin da ya haddasa fitina, da kashe kashen mutane da lalata dukiyoyi na daruruwan miliyoyin Naira, yana yawo a kan titi kamar babu abinda ya faru.
Rahoton na “Human Rights Watch” yace duk da cewa shiadu su ka kai rahoto gun 'yan sanda game da hare-hare a jihohin Kaduna da Filato, mutane kalilan kawai aka gurfanar a gaban kotu dangane da kisan dubban mutane.
Ana yawaita kiran irin wannan tashin hankali a zaman na addini a saboda kusan ko yaushe ana yinsa ne a tsakanin Musulmi da Kirista. Amma a Najeriya, bambance-bambancen kabilanci, ko tattalin arziki ko ma na siyasa dukkansu su na wakana ne ko kuma su rikide zuwa na addini.
Mai bincike kan Najeriya na kungiyar “Human Rights Watch” Eric Guttschuss, yace, “A lokuta da dama, al'ummomin da ake kai musu farmaki, kuma hukuma ta kasa bi musu kadi, sukan juya su dauki doka a hannunsu, su kai hare-haren ramuwar gayya.”
Yace a bayan kowane hari, 'yan sanda su kan tattara mutanen da suka samu a wurin, amma a lokuta da dama sukan kasa tantance wadanda suka aikata wani abu a tsakaninsu. A wasu lokutan, 'yan sanda kan nemi cin hanci kafin su yi bincike, ya kuma ce akasarin wadanda aka cuta ba su da karfin da zasu iya biyan abinda 'yan sandan ke nema.
Haka kuma, wasu al'ummomin sukan matsawa hukuma lamba a kan kada a kama 'yan kabilarsu in ji jami'in.
Yace a baya, “mun ga 'yan sanda su na bayyana fargabar kama wani ko wasu, su ma hukumomin Najeriya su na bayyana fargabar kama wasu mutanen a saboda tsoron cewa yin hakan zai haddasa wata sabuwar fitina a tsakanin wadannan al'ummomi.
Amma kuma a yayin da zaben shugaban kasa na 2015 yake kara kusantowa, wasu mazauna jihar Kaduna sun yi kashedin cewa idan har ba a kama aka hukumta wadanda suka yi kashe-kashe a 2011 ba, babu abinda zai hana zub da jini a shekarar 2015 a lokacin zabe.
Kungiyar “Human Rights Watch” ta ce ya kamata 'yan sanda su kafa wata runduna ta musamman da zata bincika tare da kama wadanda suka aikata kisan kare dangi, yayin da ita kuma gwamnatin tarayya ya kamata ta binciki dalilin da ya sa mutane kalila kawai aka hukumta ya zuwa yanzu.