Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Gwabza da 'Yan Bindiga a Yankin Karamar Hukumar Bama a Jihar Borno


Jiragen saman yakin Najeriya sun kai dauki inda suka kashe 'yan bindiga akalla 25 da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne a kauyen Ngauramari

An kashe wasu mayaka su akalla 25 da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne a wata arangama da sojojin runduna ta 7 ranar alhamis a kauyen Ngauramari dake karamar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun fito daga cikin dajin nan na Sambisa ranar alhamis da safe, sai suka ci karo da sojoji masu sintiri a kan babbar hanyar da ta taso daga Maiduguri zuwa Bama har zuwa Gwoza. An yi musanyar wuta har aka kashe wasu daga cikin 'yan bindigar a wannan lokaci.

Daga baya, jiragen saman yaki na sojan Najeriya sun kai dauki inda suka bi sawun mayakan da suka gudu har suka kashe wasu fiye da 20. An rufe wannan babbar hanyar motar na tsawon sa'o'i da dama inda aka hana motoci da mutane shigewa a yayin da ake farautar 'yan bindigar.

A cikin wannan makon kawai, ana zargin 'yan bindigar na Boko Haram da kashe mutane fiye da 20 a kan wannan babbar hanyar mota dab da kauyen na Ngauramari, wadanda suka hada da direbobi da fasinjoji.
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG