Amfanin Ilimi Ba Dan Aiki Kadai Ba Ko Dan Tarbiyantar Da 'Ya'Ya

Amina Bello Suleman

Matsalar da na fara fuskanta kasancewar ina karanta aikin jiyya shine kalmomin da ban saba jin suba sakamakon ni daga sakandire na wuce makarantar koyan aikin jiyya kai tsaye alhali wasu sai da suke je makarantun share fage kafin su sami gurbin karatun inji malama Amina Bello Suleman.

Malama Amina ta bayyana cewa an bata shawarar samun takardar tabbacin ita ‘yar asalin jihar kano ce wanda da hakan ya taimaka mata ta samun gurbin karatu a jihar.

Ta kara da cewa bayan kammala karatunta na aiki jinya, ta cigaba da karatun Unguwar Zoam, wato Midwifery, kuma bata fuskanci wata matsala ba illar mu’amala da marasa lafiya, wanda tun a makaranta aka koyar da su yadda zasu yi mu’amala da marasa lafiya.

Amina ta ce a matsayinta na ma’akaciyar jinya, an koya musu cewa marasa lafiya uzuri ake yi musu duba da irin lalurar da suke fama da ita a wannan lokaci, sannan a cewarta aiki yayi mata rana da rufin asiri a rayuwa.

Daga karshe ta ja hankalin matasa da su nemi ilimi ko ba don aiki ba domin su tarbiyantar da ‘ya’yansu a wannan zamani da ake ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

Amfanin Ilimi Ba Dan Aiki Kadai Ba Ko Dan Tarbiyantar Da 'Ya'Ya