Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce abun da ke kara mai kwarin gwiwa game da zaben wannan shekarar shi ne amincewa da amfani da na'urorin da za su taimaka wajen hana magudin zabe.
Taron gangamin yakin neman zaben da kuma raba tutucin takarar gwamnoni da 'yan majalisa na shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya da aka yi a Kaduna, ya samu halartar manyan Jam'iyyar kuma a wurin taron ne dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar NNPP, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ja hankalin talakawan Najeriya game da wannan zabe da ke tafe.
Farfesa Rufa'i Ahmed Alkali, shi ne shugaban Jam'iyyar NNPP a Najeriya, ya ce al'uma su ne alkalan kansu game da halin da Najeriya ke ciki.
Shi kuwa jigon Jam'iyyar ta NNPP, malam Buba Galadima cewa ya yi al'umar yankin arewa maso yamma su shiga taitayinsu.
Ya zuwa yanzu dai manyan Jam'iyyun Najeriya uku ne suka yi irin wannan taron yakin neman zaben a jihar Kaduna, duk kuwa da cewa Jam'iyyun da suka tsaida 'yan takarar shugaban kasa sun haura goma.
Saurari rahoton cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5