NIAMEY, NIGER - A taron manema labaran da ya kira ranar Alhamis, ministan ayyukan jinkai na Nijer Alhaji Laouan Magaji, ya yi bitar halin da ake ciki a fadin kasar sakamakon ruwan saman da aka tafka daga watannin Yuli da Agusta zuwa ranar 13 ga watan nan na Satumba.
Ya ce a duk jihohin kasar 8 ruwa yayi gyara/barna, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 137 dubban wasu kuma suka rasa matsugunnansu. Hakazalika dabbobi da dama sun mutu.
Ministan ya ce gwamnati ta samar da agajin gaggawa ga mutunen da wannan bala’in ya afkawa da dan abinda ba za a rasa ba, a saboda haka ya bukaci gudummowar kasashe da kungiyoyi masu hannu da shuni.
A yankunan da wannan al’amari ya fi muni, ambaliyar ta tilasta wa dimbin mutane tserewa zuwa makarantu a wani lokaci da ake shirin komawa ajin karatun shekarar 2022-2023, a saboda haka gwamnati ta umurci magadan gari su dauki matakai kafin zuwan ranar bude makarantu.
Saurari cikakken rahoton Souley Mumuni Barma:
Your browser doesn’t support HTML5