MC: Masu sauraronmu assalama alaikum barkanmu da sake saduwa a wannan shirin na amsoshin tambayoyinku.
Tambaya 1, 2:
Don Allah kasashe nawa ne su ke amfani da kudaden CFA, kuma kasashe nawa su ke amfani da harshen Faransanci a duniya da kuma nahiyar Afurka?
Mai tambaya:- Garba Idi Wayis Zinder, dan jihar Damagaram, mazaunin Abujan Najeriya.
Tambaya 3:
Assalama alaikum VOA Hausa, don Allah ina so ku tambaya min masana, su yi min bayanin abubuwan da ke kawo ambaliyar ruwa. A bana an samu ambaliyar ruwa sosai a sassa daban daban. Shin ko hakan na da alaka da sauyin yanayi da masana ke fada?
Amsoshin
To bari mu fara da amsar tambaya kan kasashen da ke amfani da takardar kudin CFA, da kuma wadanda ke amfani da harshen Faransanci. Idan mai tambaya Malam Garba Wayis da sauran masu saurare na tare da mu, ga amsoshin da wakiliyarmu a Damagaram, Tamar Abari, ta samo daga Malam Musa Alasan, Malamin Fasaha kuma masanin tattalin arziki a Jami’ar Andre Salifou da ke Damagaram, da Dakta Siddo Adamu, malamin Faransanci shi ma a Jami’ar ta Andre Salifou da ke Damagaram. Za a fara jin Malam Musa Alasan da bayani kan kasashen da ke amfani da takardar kudin CFA; sannan a ji Dakta Siddo Adamu da bayanin kasashen da ke amfani da kudaden CF.
Ta karshe ita ce amsar tambaya kan abubuwan da ke haddasa ambaliyar ruwa. Idan mai tambaya, Malam Saidu Abdullahi Damaturu na tare da mu, zai ji amsar da wakilinmu a Adamawa, Muhammad Salisu Lado, ya samo daga masani a fannin yanayi, Dakta Ayuba Tumba Kwabe na Kwalejin Koyar da Malanta Ta Tarayya da ke Yola, Adamawa, Najeriya.
A Saurari cikakken shirin na Amsoshin Tambayoyinku: