Ambaliyar ruwa da malalar kasa sun hallaka mutane 17 baya ga gidaje da dama da su ka ruguza a arewacin birnin Los Angeles dake jihar California ta nan Amurka, inda a watan jiya wata wutar daji ta kokkona itatuwa da ganyayen da ke kan tsaunuka.
An bayar da rahoton cewa har ila yau akwai mutane akalla 17 da suka bace yayin da a jiya Laraba aka fadada binciken gano mutanen da abin ya shafa, bayan da wata babbar tawagar bincike da ceto ta iso daga Karamar Hukumar Los Angeles da ke kusa da wurin tare kuma da taimakon dogarawan tsaron gabar Amurka da wasu karin jami’an tsaron.
“Ba mu san inda su ke ba,” a cewar wata mai magana da yawun Karamar Hukumar Santa Barbara, Amber Anderson. “Muna jin sun salwanta wani wuri cikin baraguzan.”
Yanzu haka dai mummunan hadarin nan da ya janyo gocewar kasa da safiyar ranar Talata ya lafa, wanda hakan ya ba da dama ga masu kai daukin gaggawa da ke amfani da jirage masu saukar ungulu da karnuka don su ceto mutanen da su ka makale cikin gidajensu ko kuma su ka kafe cikin laka.