Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiwuwar Aukuwar Ambaliyar Tsunami a Kudancin Pacific


New Caledonia, yankin da girgizar kasa ta auku
New Caledonia, yankin da girgizar kasa ta auku

Biyo bayan wata girgizar kasa da ta auku a New Caledonia dake yankin kudancin Pacific masu kula da irin yanayin da girgizar kasar ta haddasa suna gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar tsunami

Wata girgizar kasa mai karfin maki 7 akan ma’aunin girgizar kasa, wadda ta auku daura da yankin New Caledonia da ke Kudancin Pacific, mallakin kasar Faransa, ta haddasa wani yanayi wanda har ya sa aka yi gargadin yiwuwar aukuwar ambaliyar tsunami.

Cibiyar nazarin karkashin kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar, wadda ta auku karkashin teku ta bararraka wani wuri mai nisan kilomita 82 gabas da tsibirin Loyalty da karfe 9:43 na safe agogon yankin.

An ji duriyar igiyoyin ruwa na tsunami a New Caledonia da Vanuatu bayan da girgizar kasar ta auku tsakanin tsibirai biyu na Pacific din a yau dinnan Litini, a cewar Cibiyar Gargadin Ambaliyar Tsunami ta Yankin Pacific. Wannan ne karo na biyu na aukuwarta cikin sa’o’i wajen 12, kuma na uku tun daga watan jiya.

Dama yankin na New Caledonia wani bangare ne na abin da ake kira “Zoben Wuta,” yankin da aka faye samun girgizar kasa a wajejen na Pacific.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG