Ambaliya: Gwamnatin Borno Ta Amince A Sayo Alluran Rigakafi 400, 000 Bayan Barkewar Cutar Kwalara

Wata mai jinya rike da allurar riga-kafin Astrazeneca a Najeriya

Yayin da yake ayyana barkewar annobar a cibiyar lafiyar idanu ta Maiduguri, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Baba Gana, yace daga cikin samfur din mutane 200 da aka aike domin gwaji, an tabbatar da 17 daga ciki kwalara ce.

Ma’aikatar lafiya ta Borno ta ayyana barkewar annobar kwalara a jihar.

Yayin da yake ayyana barkewar annobar a cibiyar lafiyar idanu ta Maiduguri, kwamishinan lafiya na jihar, Farfesa Baba Gana, yace daga cikin samfur din mutane 200 da aka aike domin gwaji, an tabbatar da 17 daga ciki kwalara ce.

A cewarsa, annobar ta faru ne sanadiyar iftila’in ambaliyar ruwan baya-bayan nan da ta daidaita sassan jihar.

Farfesa Baba Gana ya zayyana kananan hukumomin Jere da Mafa da Konduga da Dikwa da kuma kwaryar birnin Maiduguri a matsayin wuraren da aka samu barkewar annobar.

Duk da cewa har yanzu ba’a samu wanda annobar ta hallaka ba, kwamishinan ya bayyana cewa ana samun karuwar yaduwar kwalarar a kananan hukumomi da dama, musamman ma da ya kasance makwabtan jihohin Adamawa da Yobe na fama da annobar.

Ya kara da cewa an samu mutane 451 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi daban-daban amma 17 kawai aka tabbatar.

Don haka gwamnatin jihar ta ayyana daukar matakan gaggawa da nufin shawo kan annobar, a yayin da hukumomin bada agaji da na ayyukan jin kai irinsu Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar likitoci na gari na kowa suka samar da wuraren da za a kwantar da mutanen da ake zargin sun kamu da cutar.