Aman Wuta Ya Nakasa Wata A Jihar Hawaii

 Hoton yadda kwale-kwalen ya lalace

Hoton yadda kwale-kwalen ya lalace

Tumbudin da wani tsauni ko dutse ya ke yi a Hawa'ii ya afkawa wani kwale-kwale dauke da 'yan yawon bude ido inda tsaunin Kilauea ke ci gaba da aman wuta.Lamarin ya jikkata mutane 23.


'Yan kwana-kwana sun ce wata mace 'yar shekaru 20 na cikin mawuyacin hali saboda ta sami karaya a cinya, sannan an kwantar da mutane 13 a asibiti, yayin da sauran aka musu jinya nan take aka sallame su.


Jami'ai sun ce fasinjojin suna cikin wani kwale-kwale ne da ke kai mutane daf da inda talgen wutar ke fita daga dutsen yana malalowa zuwa cikin tekun Fasifik.

Haka kuma, jami'an sun ce bindigar ta huda rufin kwale-kwalen, ya bar wani wagegen rami .Hakan ta lalata dakalin jirgin kwalelen.