Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba Zan Tafi Tattaunawa Da Dogon Buri Ba: Trump


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Rasha Vladimir Putin

Shugaban Amurka Donald Trump yace baya sa zuciyar za a sami wata ci gaba mai ma’ana a ganawar da zai yi da takwaran aikinsa na kasar Rasha Vladimir Putin a Helsinki.

Shugaban kasar Amurkan ya shaidawa tashar talabijin ta CBS News cewa, “ zan tafi ba tare da tsammanin wata ci gaba mai ma’ana ba, ba zan tafi da wani dogon buri ba.”

Trump yaki bayyana gurin ganawar da ta kasance irinta ta farko tsakanin shugabannin na kasashen duniya, sai dai ya yi alkawarin cewa, babu wani mugun abu da ganawar zata haifar. Trump da Putin sun tattaunawa a lokutan baya a gefen tarukan kasa da kasa.

Ganawar da Trump zai yi da Putin tazo ne bayan kwanaki uku da kwamitin bincike na musamman da Robert Mueller ke jagoranta ya tuhumi jami’an leken asirin kasar Rasha goma sha biyu, bisa zargin katsalandan a zaben shugaban kasar Amurka na shekara ta dubu biyu da goma sha shida da nufin taimakawa Trump ya lashe zaben.

Rasha bata da yarjejeniyar tasa keyar mai laifi da Amurka, sabili da haka ana shakkun zata mika jami’an ga Amurka domin a shari’anta su.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG