Allah ya yi wa tsohon kakain majalisar dokokin Najeriya Dr. Ghali Umar Na'abba rasuwa.
Marigayin ya rasu bayan fama da jinya a wani asibiti a Abuja ya na mai shekaru 65.
Ghali Na'abba wanda shaharerren dan siyasa ne ya zama kakakin majalisar wakilan Najeriya bayan dawowa dimokradiyya a 1999 inda ya rike mukamin har zuwa shekara ta 2003.
Masanin kimiyyar siyasa na jami'ar Bayero ta Kano Dr.Sa'idu Ahmed Dukawa ya ce marigayin ya bar tarihin jajircewa a harkokin shugabanci inda ya yi tsayin dakan hana majalisar wakilai zama 'yar amshin shatan sashen zartarwa a wa'adin farko na mulkin Olusegun Obasanjo.
Tuni a ka shiga mika sakon ta'aziyyar rasuwar marigayin wanda haifaffen jihar Kano ne.
Bayanai na nuna za a gudanar da jana'izar a Kano yau din nan Laraba.