Alhazai A Kasar Saudiya Na Shirye-shiryen Fara Aikin Hajji Da Hawan Arfa

ABUJA: Hajj 2017

Jami’an Hukumomin Alhazai sun garzaya zuwa Mina, Arfa da Muzdalifa don tabbatar da komai na tafiya daidai gabanin fara aikin Hajjin nan da sati guda.

ABUJA, NIGERIA - Da alamu bana an samu karin Alhazai fiye da shekarun baya yayin da aka samu dubban mutane daga kasashe daban-daban a fadin duniya da suke kasa mai tsarki don sauke farali, inda Najeriya ke da maniyyata fiye da dubu sittin (60,000).

Hukumar Alhazan Najeriya Ta Bukaci Maniyyata Da Su Ba Da Kudin Ajiya

Wannan dai ya sa Hukumar Alhazai ta Najeriya NAHCON da sauran wakilan Hukumar na jihohi suka kai ziyara filin Arfa da sauran wurare don tabbatar an bin tsarin yadda za’ayi jigilar Alhazai cikin sauki ba tare da samun cunkuso ba.

Da yake bayani a lokacin ziyarar, mai kula da jigilar Alhazai a kamfanin masu yin hidima ga Alhazai na kasashen Afrika wadanda ba Larabawa ba, Abubakar Banama ya ce zasu jajirce wajen tabbatar da cewa an ware wa kowace jiha ta Najeriya motar da za ta yi jigilar Alhazan ta zuwa wadannan wurare akan lokaci.

NAHCON - Hukumar Alhazan Najeriya

A nasa bangaren mai kula da zirga-zirgan Alhazai na hukumar NAHCON Dr. Aliyu Tanko ya ce makasudin kai ziyara shine don tabbatar da cewa komai ya tafi yadda aka tsara ba tare da an cutar da kowa ba.

Mataimakin shugaban kula da harkokin aikin Hajji na jihar Yobe Muhammad Nasir Yusuf ya ce wannan wani ci gaba ne da aka samu kuma zasu tabbatar sun wayar da kan Alhazansu don ganin sun yi abinda ya dace.

Idan za’a iya tunawa a lokacin aikin Hajji na shekarar 2015 an samu turereniya inda mutane suka rasa rayukansu, sai dai tun daga lokacin an samu gyare-gyare ta yadda ba’a bari mutane suje waje sai an yi tsari.

Saurari cikakken rahoton Hauwa Umar:

Your browser doesn’t support HTML5

Alhazai A Kasar Saudiya Na Shirye-shiryen Fara Aikin Hajji Da Hawan Arfa .mp3