Azawa Muhamman, wakilin ofishin dake tallafawa ‘yan gudun hijira na majalisar dinkin duniya dake garin Arlit a jihar Agadez ya tabbatar da cewa bakin sun kai 318 da aka kai garin Assamaka dake cikin jihar Agadez, inda reshen hukumar dinkin duniya da sauran masu aiki a Assamaka suka taimaka masu.
Azawa, ya kara da cewa yawancin ‘yan gudun hijirar sun fito ne daga kasashen Afrika ta yamma da suka hada da, Guinea, da Senegal, da Kamaru, da Mali, da Najeriya, da Ivory Coast, da kuma janhuryar Benin.
A duk lokacin da wata kasa ta koro bakin haure, sukan sami kansu cikin wani mawuyacin hali, kamar yadda wadannan ‘yan gudun hijirar da aka ceto daga Assamaka suka sami kansu a ciki.
Azawa, ya kuma ce, yawancin bakin sun galabaita saboda tafiyar da suka sha da kafa. Ruwa, abinci da magunguna sune muhimman abubuwan da aka taimakawa ‘yan gudun hijir da su, daga nan aka sanya su a cikin mota zuwa Agadez inda ake raba su zuwa wasu garuruwa.
Bisa ga abubuwan dake faruwa ana iya cewa garagadin da gwamnatin Nijar ta yiwa makwabciyarta, kasar Algeria akan ta daina jibge mata bakin haure ‘yan Afrika akan iyakarta bai kai ga kunnuwan ta ba. Yanzu dai an zuba ido a ga yadda hukumomin Nijar zasu bullowa wannan lamarin.
Za ku ji karin bayani a cikin wannan rahoton na wakilin sashen hausa, Haruna Mammane Bako.
Your browser doesn’t support HTML5