Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaman Lafiya Na Dada Tabbata Tsakanin Habasha Da Eritiriya


Shugaban Eritiriya Isaias Afwerki da Firaministan Habasha Abiy Ahmed
Shugaban Eritiriya Isaias Afwerki da Firaministan Habasha Abiy Ahmed

Hulda tsakanin kasashen Habasha da Eritiriya sai kara inganta ta ke yi. Ko a karshen makon nan, sai da shi ma Shugaban Eritiriya ya kai ziyara kasar Habasha, inda zai yi kwanaki uku ya kuma bude ofishin jakadancin kasarsa.

Shugaban Eritiriya (Eritrea) isa kasar Habasha a cigaba da daukar matakan kawo karshen fafatawar da kasashen biyu su ka kwashe shekaru 20 su na yi.

Ana kyautata zaton Isaias Afwerki zai yi kwanaki uku a kasar ta Habasha, inda zai sake bude ofishin Jakadancin kasar ta Eritrea a birnin Addis Ababa a gobe Litini sannan ya kuma ziyarci wani babban kamfani.

A makon jiya shi ma Firaministan Habasha Abiy Ahmed ya je kasar ta Eritrea inda shugabanni biyu su ka rattaba hannu kan yarjajjeniyar sake bude ofisoshin jakadancinsu, da maido da huldodin wasanni da diflomasiyya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG