Shugaba Mauricio Macri mai ra’ayin rikau ya amince da shan kaye a zaben Argentina jiya da daddare, wanda hakan ya share fage ga masu sassaucin ra’ayi su sake dawowa kan karagar mulki karkashin, Alberto Fernandez, bayan da mafusatan masu jefa kuri’a suka yi watsi da yadda shugaban kasar tinkarar zazzafar matsalar tattalin arzikin kasar wadda ta jefa mutane da dama cikin talauci.
Sakamakon zaben ya haifar da dawowar tsohuwar shugabar kasar Cristina Fernandez tamkar almara, wadda yanzu ita ce Mataimakiyar shugaban kasa ga Alberto Fernandez, wadda a da ita ce shugabar shi, kuma abin da masu suka suke cewa hakan ne musabbabin tasirin mulkinsa.
Macri ya fadawa taron magoya bayansa a shedkwatar yakin neman zabensa cewa ya kirawo Alberto Fernandez don ya taya shi murna kuma ya gayyace shi don su yi Karin kumallon safe su tattauna a yau Litinin a fadar shugaban kasa ta Pink.