WASHINGTON D C —
Daruruwan masu zanga zanga a Iraqi sun ci gaba da gudanar da gangamin nuna kin jinin gwamnatin kasar a yau Lahadi a babban filin Tahrir dake birnin Baghadaza.
An kashe masu zanga zanga fiye da 60 sakamakon arangamar da ta faru da ‘yan sanda tun bayan barkewar zanga zangar a makon da ya gabata.
“Mun zo nan ne don mu ga bayan gwamnatin baki daya, a cewar daya daga cikin masu zanga zangar.
A wata sanarwa yau Lahadi, hukumar yaki da ‘yan ta’adda ta Iraqi ta fadi cewa an kai jami’an hukumar yankin don su kare gine-ginen gwamnati daga tsagera marasa da’a.
Tawagar jami’an ta ce an ba ta umurnin ta yi amfani da duk matakan da suka dace don kawo karshen zanga zangar nuna kin jinin gwamnatin firayin minista Abdel Abdul Mahdi.
Facebook Forum