Alakanta Yakin Neman Zabena Da Rasha Bita Da Kullin Siyasa ne:Tump

Donald Trump Jr da lauya 'yar kasar Rasha Natalia

Shugaban Amurka Donald Trump ya sake sabunta ikirarinsa na cewa zargin kwamitin yakin neman zabensa da ake yi da wata alaka da kasar Rasha, ba wani abu bane face bita da kulli irin wanda ba a taba gani ba a tarihin siyasa.

Ya bayyana haka ne a sakonsa na twitter kwana daya bayanda babban dansa, Donald Trump Jr, ya bayyana wadansu sakonnin email da suka nuna yadda shi da wadansu manyan jami’an yakin neman zaben Trump suka gana da wata lauya 'yar kasar Rasha, wadda ta yi musu tayin bayanan batunci kan abokiyar hamayyarsu, ‘yar takarar shugaban kasar Amurka ta jam’iyar Democrat Hillary Clinton.

Donald Trump Jr ya fada a wata hira da tashar talabijin ta Fox News jiya Talata cewa, bai fadawa mahaifinsa wannan ganawa da aka yi ba, ya kuma yi watsi da zargin cewa akwai hadin baki tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump da Rasha a matsayin shirme.

Wakilan Muryar Amurka a majalisar dokoki sun ce jin cewa, Donald Trump Jr, ya nemi bayanan batanci kan Clinton kafin zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba ya girgiza ‘yan majalisa, ya kuma haifar da martani mai zafi, musannan daga ‘yan jam’iyyar Democrat.