Shugaban Amurka Donald Trump ya fada jiya Lahadi cewa, sau biyu yana "matsawa" shugaban Rasha Vladimir Putin game da katsalandan da aka yi zargin Rashar ta yi a zaben Amurkaa bara.
Dalilin hakan, Trump ya ce, yanzu lokaci ya yi, da ya kamata "a maida hankali domin ci gaba wajen aiki mai ma'ana da hukumomin Rasha dake Moscow."
A jerin sakonnin Twitter da ya aike bayan da ya dawo daga taron kolin kunigyar kasashe masu arziki da ake kiraG20 da aka yi a Jamus, Mr. Trump ya ce Shugaba Putin ya musa cewa kasarsa ta na da hannu wajen yin shishishigi a zaben Amurka.
Shugaban na Amurka ya ce shi da takwaran aikinsa, sun tattauna kan "kafa sashe na musamman kan tsaro mai tsanani a yanar gizo ko internet, domin hana aikata wasu miyagun ayyuka da kuma kare wa."
Wasu jiga-jigan majalisar dokokin Amurka karkashin jam'iyyarta Republican, sun yi shagube da shawarar Trump na aiki tare da Rasha kan tsaro a internet.
Sanata Lindsey Graham, ya fada a cikin shirin tashar talabinjin na NBC da ake kira "meet the Press, wannan ba shi ne shawara mara ma'ana da ya taba ji ba, amma ta kusan zama haka."
To amma shi kuma shugaban ma'aikata a fadar WhiteReince Preibus, ya fadawa tashar talabijin ta Fox cewa, "ko kusa" Trump bai amince da furucin shugaba Putin ya yi cewa kasar sa ba ta yi katsalanda a zaben na Amurka ba.
Facebook Forum