Kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya wato IPMAN ta ce tabbas an fara ganin dogayen layukan mai kuma hakan baya rasa nasaba da furucin shugaba Tinubu amma sai mambobinta sun sayo mai daga NNPCL din a yau kafin ta iya magana a kan batun karin farashin da za a iya gani, lamarin da ya fara sanya fargaba a zukatan yan kasa.
Jim kadan bayan ayyana janye tallafin man fetur da sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi a jawabinsa bayan rantsar da shi ne aka fara ganin dogayen layukan mai a birnin tarayya Abuja da wasu sassan kasar duk da cewa yan kasar sun yi marhaban da matakin da Tinubun ya sanar a ranar Litinin din.
Shin ‘yan kasa sun fahimci me ake nufi da janye tallafin man fetur din nan kuwa, Fitacciyar lauya, ’yar kasuwa, kuma jagoriya a wata gidauniyar tallafa wa lafiyar mata, Rahama Bungudu, ta ce da yawa cikin ‘yan Najeriya ba su fahimci me ake nufi da cire tallafin ba saboda tun farko ba a san ya aka yi aka samo shi ba.
Tuni dai wasu ‘yan Najeriya ma suka fara tofa albarkacin bakinsu a game da lamarin inda wasu ke ganin cewa bai kamata a dora laifin dogayen layuka da aka fara gani a kan gwamnati ba illa ‘yan kasuwa ne suka fara boye man don cin kazamar riba wasu kuma ke cewa ‘yan kasa ne suke nuna fargabar sayen mai suna karfafa wa ‘yan kasuwa wajen boyewa.
Mal. Abubakar Maigandi DakinGari, shi ne mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya, kuma ya bayyana cewa tabbas an fara ganin bayyanar dogayen layukan mai a sassan kasar daban-daban wanda baya rasa nasaba da furucin sabon shugaban kasa Bola Tinubu na janye tallafin man fetur, yana mai cewa a yanzu dai sai mambobinsu sun sayi mai daga depot-depot din kamfanin NNPCL kafin yan kasuwa su san irin karin da za su iya yi a farashin kowace litar mai.
Da muka tuntubi kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya a kan wannan al’amari na dogayen layin mai da aka fara gani, babban jami’in yada labarai da hulda da jama’a na kamfanin, Mal. GarbaDeen Muhammad, ya ce kar ‘yan kasa su shiga fargaba saboda akwai wadataccen man da zai ishe su na kiminin nan da kwanaki 30.
A wani bangare kuwa, a cikin wata sanarwa da shugabanta Festus Osifo da babban sakatare, Nuhu Toro suka sanya wa hannu, kungiyar ma’aikatan kamfanoni ta Najeriya wato TUC ta bayyana cewa sabon shugaban kasa Bola Tinubu ba zai iya daukar matakin cire tallafin man fetur shi kadai ba kuma kamata ya yi ya dakata na dan lokaci don ba da damar tattaunawa mai karfi da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki, kafin yanke shawara kan batun janye tallafin man fetur a kasar.
Kungiyar TUC ta kara da cewa akwai batutuwa da dama da ya kamata a yi la’akari da su cikin ruwan sanyi da kuma warware su kafin shugaban ya yanke irin wannan shawara.
Idan Ana iya tunawa dai tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya sha jaddada wa yan kasar cewa za a janye tallafin man fetur a watan Yunin da za a shiga kuma ya kara karfafa batun a watan Afrilun da ya gabata kuma masana sun ce bai kamata batun cire tallafin da sabon shugaba Tinubu ya yi a jawabinsa na ranar 29 ga watan Mayun ya shammaci yan kasa ba saidai kamata ya yi gwamnatin ta dauki dukkan matakan da suka dace don kawo sauki ga talaka a kasar.
Saurari rahoton Halima Abdulra'uf
Your browser doesn’t support HTML5