‘Yan majalisar dattawan Najeriya masu goyon bayan Sanata Ahmad Lawan daya nemi shugabancin majalisar da wasu ‘yayan jam’iyyar APC na ci gaba da bayyana shakku kan samun goyon bayan shugabancin majalisar dokokin Najeriya ga kudirori da bukatun da shugaba Muhammadu Buhari zai rinka gabatarwa majalisar kasar.
Sanata Barau Jibrin, mai wakiltan Kano ta arewa, yace “ Duk inda mutun ya nemi ya zama shugaba in ya zamana baida gaskiya, baida Amana bai bin ka’idodin in an shirya abu da shi bazai bi tsarin da aka shirya ba to gaskiya bai dace da shugabanci ba, al’umar Najeriya,sun zabi jam’iyyar APC,wace tasamu shugaban kasa kuma ta samu rijaye a majalisun dattijai dana wakilai, to kamata yayi ace duk wani wanda zai fito ya zama shugaba ya zama dan jam’iyyar, kuma ya tafi da tsarin APC, in wani yayi wani abu sabanin wannan to gaskiya Magana yayi abu sabanin abun da ya dace.”
Sanata Barau Jibrin ya kara da cewa´ “Koda hedkwatar PDP, aka dasa a majalisa bazai hana muyin aikin mu ba, bazai hana muyi abun da ya dace da al’umar muba, amma tarnaki kuwa dole ne a samu akan yadda ake son a gudanar da aiki ta yadda za’a kwato dukiyar mutane da aka sace tunda yake yanzu PDP, din ce ta riga ta kafa shugabanci a wadannan majalisu guda biyu.”