Yaki da ‘yan ta’adda na Boko Haram, shine babban batun da ya mamaye taron ranar Sojoji.
Tsohon kwamamdan dake yaki da Boko Haram, na “Operation Lafiya Dole” Manjo Janar Leo Irabor, shine ya gabatar da kasida.
Inda yake cewa an tabbatar da kwanciyar hankalin siyasa a shiyar arewa maso gabashin Najeriya ta hanyar ragargazar ‘yan ta’adda na Boko Haram a yankin, yana mai cewa nasarar ya sa a yanzu haka duk matakai na gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi suna hedkwatocinsu suna gudanar da aikin su.
Janar Irabor, yace wannan hubbasa na Sojojin Najeriya, ya kuma kawo habaka tattalin arziki a yankin, yana mai cewa batun tattalin arziki na nufin maiido da hada hadar tattali arziki nay au da kullum a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.
Ga wadanda suka san Yobe da Adamawa a baya yanzu kuwa batun tsaro sai godiya sai dai ga jihar Borno nan ma duk ta gomashin tsaro amma da sauran rina a kaba duk cewa an ‘yanto dukka sassan jihar har yanzu akwai sauran da burbushin aikace aikacen mayakan Boko Haram.
Your browser doesn’t support HTML5