Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kai wa Dakarun Nijar Harin Kwantan-Bauna


Sojojin Nijar a kan iyaka
Sojojin Nijar a kan iyaka

Akalla dakarun Jamhuriyar Nijar 10 ne suka bace bayan wani hari da wasu 'yan bindiga da ake tunanin masu tsatsauran kishin Islama ne suka kai a yankin Midale dake jihar Tahoua.

Wasu mahara da ake zargin daga Mali suke, sun kai hari akan sojojin Nijar inda suka kashe dakarun kasar biyar suka kuma jikkata wasu shida.

Da misalin karfe goma na safiyar jiya ne wasu da ake kyautata zaton masu tsatsaurin kishin Islama ne dake aikata ta'addanci a Mali suka afkawa sojojin Nijar dake tsaron kan iyakar kasashen biyu a garin Midal dake cikin gundumar Tasara ta jihar Tawa.

Sojojin Nijar suna sintiri ne domin yakar masu safarar muggana makamai da kwayoyi.

A harin sojojin Nijar biyar ne suka rasu kana shida suka jikkata yayin da wasu 10 suka bace kamar yadda wani dan jarida dake yankin ya tabbatarwa da Sashen Hausa na Muryar Amurka.

Ga rahoton Haruna Mamane Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG