Akwai Sabanin Ra'ayi Akan Neman Sulhu da Tsagerun Niger Delta

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

Shugaban Najeriya Muhammad Buhari na neman kawo karshen tashin tshinar da 'yan tsagerun yankin Niger Delta ke haddasawa lamarin da ya shafi tattalin arzikin kasar.

Gwamnatin tarayyar Najeriya na kokarin zaman teburin sulhu da 'yan tsagerun Niger Delta dake yankin kasar mai arzikin man fetur.

To amma an samu rarrabuwar kawumna a sakamakon wannan lamari. Wasu na ganin zama da 'yan tsagerun shi ya fi dacewa. Wasu kuma suna ganin yin hakan zai kara rura wutar tsageranci.

Wasu na ganin maimakon a cigaba da yin fito na fito tsakanin tsagerun da sojojin Najeriya hanyar da ta fi dacewa ita ce a zauna dasu a tattauna. Wani basaraken yankin Godspower Gbeneken yana daga cikin masu irin wannan ra'ayin. Yace matakin soja ba shi ne mafi dacewa ba, kuma ba zai taba zama zabin da ya dace ba.

Amma wasu kuma na ganin cewa tattaunawa da 'yan tsageran zata sa wasu daga yankin su dauki makamai domin su ma su samu kudin fansa daga gwamnati. Wani Anthony Ogenejabor wanda lauya ne a birnin Benin yana da irin wannan ra'ayin. Yace da a ce shi ba lauya ba ne kuma mazaunin yankin Niger Delta ne sai ya kafa tasa kungiyar tsagerancin domin gwamnati ta nemi yin sulhu dashi ta kuma biyashi kudin fansa. Yace shi bai ga anfanin yin sulhu dasu ba.

Wannan yunkurin na gwamnatin tarayya ba shi karon farko ba da gwamnatin zata nemi sulhu da 'yan tsagerun yankin. A shekarar 2009 gwamnatin tarayya ta dauki matakin biyan tsagerun ta hanyar sama masu aiki da horar dasu a fannonin rayuwa ta yau da kullum domin kawai a samu zaman lafiya.

Tattaunawa da kungiyar da ake kira Niger Delta Avengers ana iya cewa ta fara haifar da da mai ido kamar yadda wani jami'in kasar ya shaidawa Muryar Amurka cewa sun amince su dakatar da bude wuta amma daga baya kungiyar ta karyata batun.

Yanzu haka watannin da kungiyar ta kwashe tana kai hari kan bututun mai da wasu mahimman kadarorin kamfanin man fetur na kasar ya haifar da raguwar man da kasar take hakowa da kusan rabi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Sabanin Ra'ayi Akan Neman Sulhu da Tsagerun Niger Delta - 2' 28"