Wani lokaci ‘yan ta'addan kan kai hari sansanonin sojojin kuma kai tsaye suke isa zuwa ga wajen aje makamai da ma motocin yaki suyi awon gaba dasu, abin dake aza ayar tambaya ta yaya ‘yan ta'addan ke samun bayanan da ke basu kwarin gwiwar aikata irin wannan ta'asa.
An dai sha kama wasu daidaikun sojoji na hada baki da yan ta'addan AISWAP da Boko Haram a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, misali ko a watan jiya an kama wani soja mai suna Kofur Jibrin Mohammed dake aiki a wata bataliyar soji dake garin Gaidam kan iyakar Najeriya da Nijar a jihar Yobe na hada baki da yan ta'addan.
Sojan wanda wani binciken sojojin ya kai ga gano tare da kamo shi bayan ya sulale daga bakin aiki, a kan hanyar kaishi wajen bincike ya kwace bindigar wani sojan da suka kamoshi ya harbe kansa.
Ko da gabanin haka ma an sha kama sojoji tsiraru na hada baki tare da aiki tare da ‘yan ta'addan Boko Haram ko ‘yan bindiga dadi a shiyyoyin Arewa maso gabas da Arewa maso yamma, abin da ta kai a watannin baya har rundunar tsaron kasar ta aike da wasu takardun gargadi ga rundunonin sojin kasar.
Ko a wannan karo ma babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriyar Janaral Lucku Irabor ya magantu a kan al'amarin a wata zantawa da ya yi da manema labarai a hedkwatar tsaron kasar dake Abuja inda ya ce suna da tsari na cikin gida da suke gano tare da kamo sojin dake hada kai da makiya,
Janaral Irabor ya ce ai duk sojojin da ake kamawa ba wai rahotonsu ake kai masu ba, a'a sune da kansu ke bankadosu, kuma ana daukar matakan ladabtarwa a kan su domin ba wata rundunar soji da bata da kotun soja da ake kira COURT MARSHALL.
Duk da a wasu lokuta ana ta maganganu kan haklkin bil'adama, to amma a tsari irin na sojoji inji babban Hafsan, bai da muhalli a gidan soja, domin su suna da tsarin su na soji, kuma da'a babban ginshiki ne a wajensu, duk kuma inda aka ce ba da'a toh ba soja.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja.
Your browser doesn’t support HTML5