Akwai Matukar Alfanu Wajen Tarbiyantar da Yara Kanana

  • Ibrahim Garba

Wani taron ankarar da matasa game da rayuwa mai kyau.

Wata kwararrar mai ilimin zamantakewa da halayyan dan adam (sociologist) ta ce irin tarbiyyar da al'umma ta ba da matasanta za ta shata rayuwarsu da ta al'ummar kasar nan gaba.
Wata kwararrar mai ilimin zamantakewa da halayyan dan adam mai suna Malama Zainab Sa'id Kabir, ta ce jihohin Arewacin Nijeriya sun yi kokari ta fuskar daukar matakan kawar da al’adar bara da almajiranci da kuma safarar yara daga wannan jiha zuwa waccen da kuma sauran matakan inganta rayuwar matasa. To amma ta ce idan ana da kyau ya kamata a kara da wanka.

Malamar, wadda ke koyarwa a Jami'ar Bayero da ke Kano ta arewacin Nijeriya, amma kuma a yanzu ta ke kara ilimi a Jami'ar Ohio ta Athens a nan Amurka, ta yi kira ga shugabanni a dukkan matakan shugabanci su tabbatar ana aiwatar da kudurorin da aka cimma na inganta rayuwar yara kanana musamma ma irin na bai daya. Ta ce ko da mutane sun jahilci wata hayar inganta rayuwar yara ko na al’umma baki daya bai kamata shugabanni su ki aiwatar da it aba don kawai su burge wadanda su ka jahilci alfanun abin. Wannan, in ji ta, shi ne ma banbancin shugabanni da sauran mutane.

Da ta juya kan iyaye sai Malama Zainab ta yi kira garesu da su himmantu wajen tarbiyantar da ‘ya’yansu saboda su ne na farko da aka dora masu nawayan kula da ‘ya’yansu kafin al’umma baki daya. Ta ce bai kamata iyaye su yi wasa wajen samar da abinci ba. Haka ma batun ilimantarwa da koyar da sana’a da dai sauran su.
Daga karshe masaniyar zamantakewa da halayyar dan adam din (sociologist) ta yi gargadin cewa muddun ba a dau batun kyautata rayuwar yara kanana da kuma tarbiyantar da su da muhimmanci ba, to za a fuskanci sakamako mara kyau a karshe.

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Matukar Alfanu Wajen Tarbiyantar da Yara Kanana -