Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Amince Da Kara Wa'adin Dokar Ta Baci


Dakarun aiwatar da dokar ta baci
Dakarun aiwatar da dokar ta baci

Bayan da majalisar wakilan Najeriya ta gana a kebe da manyan jami'an tsaron kasar ta amince da kara wa'adin dokar ta baci da shugaba Jonathan ya nema.

Majalisar Wakilan Najeriya ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a jihohi uku dake arewa maso gabashin kasar kamar yadda shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nema.

Amincewar ta majalisar da bukatar ta biyo bayan ganawa da 'yan majalisar suka yi a kebe da manyan jami'an tsaron kasar. Air Vice Marshall Ola Sa'ad yana daya daga cikin manyan jami'an tsaro da majalisar ta gana dasu inda ya ce karin wa'adin dokar ta bacin ya bito bayan bukatar shugaban kasa ne domin inganta tsaro a jihohi ukun nan na arewa maso gabas. Ola Sa'ad ya ce idan an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihohin uku kamar yadda ake samu a wasu bangarorin Najeriya to ba za'a bata lokaci ba za'a dage dokar.

Sai dai dan majalisa Aliyu Gebi daga jihar Bauchi ya ce a dunkule a matsayinsu na majalisa sun yadda, amma shi a matsayinsa na mai wakiltar Bauchi ta tsakiya yana gani sun yi gaggawan yadda. Ya bada wasu dalilai. Ya ce na daya basu bincika abubuwan da aka gaya masu ba na neman karin wa'adin. Na biyu akwai rahotannin yadda ake cin zarafin bil adama a jihohin da dokar ta shafa. A bangaren jami'an tsaro akwai wasu kayan aiki da basu da shi. Ya ce a cikin karin wata shidan ne za'a kawo masu kayan aikin da suke bukata?

Shi kuwa Sanato Ahmed Zanna daga jihar Borno ya bayyana dalilan da suka sa suka amince da karin wa'adin. Na farko ya ce sun san sojoji basu yi aiki kamar yadda ya kamata ba. Ya ce a yanayin da suka samu kansu ba zata yiwu mutanen Borno su kare kansu da kansu ba sai da sojojin. Don haka basu da wata zabi sai dai su amince da bukatar shugaban kasa domin 'yan Boko Haram AK 47 suke yawo da ita. Su goma kawai na iya hallaka daruruwan mutane.

Madina Dauda nada karin bayani.

Majalisar Wakilan Najeriya Ta Amince Da Kara Wa'adin Dokar Ta Baci - 2:56
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG