Abunbuwan da sarakunan suka tattauna a kai sun hada da batun makiyaya da manoma da batun rikicin filaye da shan kwaya da kabilanci da ma ban-bancin addini. Wadannan abubuwa ne da ma wasu matasa a jihar Adamawa suka kuduri aniyar yaka domin samun zaman lafiya da cigaba a jihar dama kasar Najeriya.
A taron gangami da sarakunan suka yi sun ambato batun shan kwaya a matsayin wani babban bala'i da ya addabi jihar da kuma ya ke jawo fitinu a tsakanin al'umma. Malami Guda Abba sarkin matasan masarautan Ganye ya ce bayan batun shan kwaya wani batu kuma dake ci masu tuwo a kwarya shi ne batun rikici tsakanin makiyaya da manoma a masarautarsa kodayake akwai matakan da suke dauka.
Mr. Jatu John sarkin matasan kasar Bula ya bayyana yadda suke warware takaddama tsakanin makiyaya da manoma. Ya ce sun tattauna bangarorin biyu har suka samu masalaha abun da ya kawo karshen irin wannan matsalar.
Hukumar yaki da sha ko fataucin miyagun kwaya, watoi NDLEA a takaice, ta tura jami'inta wurin taron. Alhaji Abdulkadiri Abdullahi Fakai da ya wakilci kwamandan jihar ya yaba da taron tare da matakan da sarakunan matasan ke dauka. Babban Sakataren sashen wayar da al'umma a jihar Alhaji Mustapha Raji shi ne ya wakilci gwamnan jihar Murtala Nyako.
Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.