Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya ce duk da yake lamarin ba wata muguwar matsala bace, amma akwai bukatar yin sulhu tsakanin bangarorin, ya kara da cewa idan an sami rashin fahimta kamata yayi a zauna a nemi sasanci da juna.
Akwai kwamiti da shugaban kasa ya kafa wanda mataimakin shugaban kasa yake jagoranta, dan haka zasu kira kowa da kowa domin a zauna a yi sasanci.
Gwamnan wanda ke ci gaba da rangadi a kananan hukumomin jiharsa, a karshen makon nan ya ziyarci kananan hukumomin Bidda da Bako, kuma talakawan yankunan sun bayyana farin cikinsu musamman yadda gwamnan ya ganewa idanunsa irin matsalolin da jama’a ke fama da su, kama daga rashin tsabtataccen ruwan sha, zuwa wutar lantarki.
Alhaji Abubakar Sani Bello, ya sha alwashin samar da ababen more rayuwa a tsakanin al’ummar kananan hukumomin jihar.
Daga karshe gwamnan ya mayar da martani akan wani bidiyo dake yawo a yanar gizo wanda ke nuna lokacin da jama’a ke jifan tsohon gwamnan jihar da duwatsu wanda jama’a da dama suka yi tunanin gwamnan mai mulki yanzu ne.
Mustapha Nasiru Batsari nada karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5