Akwai Bukatar Duba Tsarin Shari’a A Najeriya - Masana

Kotu

Yayin da a Najeriya ake fuskantar kalubale da suka shafi laifukan fyade da cin zarafin mata da kananan yara da sauran kasha-kashe marasa dalili, masana harkokin shari’a a matakai daban-daban na ganin yadda tsarin shari’ar kasar ya ci karo da al’adu, yanayin zamantakewa da kuma addini.

Wannan al’amarin dai ya sake kunno kai ne a daidai lokacin da ake ganin cewa masu aikata muggan laifuffuka kamar fyade, cin zarrafin mata da kananan yara, kashe-kashen mutane na ci gaba da cin karen su ba babbaka sakamakon yadda ake daukan tsawon lokaci wajen zartar da hukunci, lamarin da ke sanyaya wa wadanda aka zalunta gwiwa har ya kai ga suna yafewa masu laifin.

A bisa ga dukkan alamu neman daidaito a sha’anin kawo karshen aikata muggan laifuka a Najeriya, ta hanyar hukunta masu aikata su na bukatar dukannin masu ruwa da tsaki su hada gwiwa don warware matsalolin baki daya.

A jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya, Kwamishinar Harkokin Mata a jihar, Hajiya Hauwa Baa Abubakar, ta ce a kusan dukkan gundumomin jiharta an kafa kotuna na musamman don tabbatar da cewa an hukunta duk wanda aka kama da aikata muggan laifuka ba tare da bata lokaci ba.

A can jihar Zamfara kuwa, kwamishinan shari’a kuma antoni janar na jihar Zamfara, Malam Aminu Junaidu, ya bayyana cewa musifar da ke mayar da hannun agogo baya a wajen hukunta masu aikata laifuffuka, kamar na fyade da cin zarrafi shi ne yadda wadanda aka ci zarrafinsu ke jin kunyar bada shaida a kotuna, duk da cewa gwamnatin jihar ta amince da dokar nan ta hukunta masu aikata muggan laifuffuka a wani mataki na tabbatar kawo karshen wannan al’amari.

Baya ga matakan da aka yi ta dauka a jihohi, shin a ina ne matsalar take, fitaccen lauya barista Mainasara Kogo, ya ce tsarin shari’a da ake amfani da shi da ya sabawa al’adu, yanayin zamantakewa, mutunci da addinin ‘yan Najeriya na daga cikin dalilan da ya sa matsalar aikata muggan laifuffuka ta ki ci ta ki cinyewa.

Masana a Najeriya dai na ganin cewa kamata ya yi a bada karfi ga yadda dukkannin masu ruwa da tsaki, za su hada gwiwa don fahimtar yadda lamarin yake don yin nazarin da zai kawo mafita mai dorewa a yaki da miyagun laifuffuka a kasar.

Domin Karin bayani saurari rahotan Halima Abdulrauf:

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Bukatar Duba Tsarin Shari’a A Najeriya - Masana - 3'59"