Hukumar kididdiga ta kasa NBS a Najeriya, ta ce farashin kayan masarufi ya karu a watan Nuwamban da ya shude idan aka kwatanta da farashinsa a watan Nuwambar bara.
Cikin wani rahoto da ta fitar a Abuja, wanda ya duba wasu daga cikin farashin kayayyaki, hukumar ta ce kilo daya na nama da ba kashi, ya karu da kashi 29.
Hakan na nufin farashin naman ya tashi daga naira 1,812 a watan Nuwamban bara zuwa naira 2,337 a watan Nuwamban bana.
Rahoton ya kara da cewa, kilo daya na shinkafar gida ya karu da kashi 18.95.
Hakan na nufin farashin ya karu daga naira 421 a watan Nuwamban bara zuwa naira 500.80 a watan Nuwambar 2022.
Hukumar ta kara da cewa, kilo daya na tumatir ya karu da kashi 0.15, abin da ya sa aka sayar da shi naira 454.46 a watan Nuwambar bana.
Sannan farashin kilo daya na wake, ya haura daga naira 490.19 a watan Nuwambar bara zuwa naira 578.55 a watan Nuwamban bana.