Darektan cibiyar yaki da masu liken asiri da tsaro ta kasa, William Evanina ya ce ma’aikatar tattara bayanan sirrin Amurka ta fada cewa kasashen ukun sun dukufa wurin rarraba kawunan Amurka da kuma lalata harkokin demokararadiyar Amurkawa.
Amma ya ce Rasha da China da kuma Iran sun samu sabani a kan mutumin da suke so su ga ya lashe zaben shugaban kasa a cikin watan Nuwamba tsakanin shugaban Donald Trump da abokin karawar sa na Democrat, mataimakin shugaban kasa Joe Biden.
Mun gano cewa Rasha tana daukar matakai da dama na zubarwa mataimakin shugaban kasa Joe Biden da mutunci da ma ma jami’iyar Democrat da take mata kallon abokiyar gabar Rasha, inji Evanina a wata sanarwa ta yammacin jiya Juma’a, inda ya ce yunkurin Moscow ya yi daidai da sukar da Kremlin ke yiwa Biden da tsohon shugaba Barack Obama.