Akalla Mutane 53 suka rasu a wani hadarin mota a kasar Ghana

Kintampo, Ghana, wurin da hadarin mota ya faru

Hukumomin kasar Ghana sun bada sanarwar aukuwar wani mummunan hadarin mota da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da hamsin

Hukumomin kasar Ghana sun ce akalla mutane 53 sun rasa rayukansu a lokacin da wata motar bas da kuma wata motar daukar kaya suka yi karo da junaa kan wata babbar hanya dake arewa da Accra, babban birnin kasar a daren jiya laraba.

A safiyar yau ne shugaban kasar Ghana John Mahama ya rubuta sakon ta’aziyya a shafin sa na twitter, ya kuma ce ma’aikatan agaji na kan aikin ceto mutane daga wajen da hadarin ya auku a Kintampo, da ke yankin Brong Ahafo.

Ana tunanin wannan shine hadarin mota mafi muni da Ghana ta taba gani cikin shekaru da dama da suka wuce.

Rahotanni sun nuna cewa, Motar kirar bus dauke da pasinjoji 42, ta kara da wata mota dake tahowa, abinda ya sa motoci da yawa karawa. An kuma ce wasu su 23 sun jikkata