Bisa ga dabi'ar dan adam yaka tsoraci duk wani abu da bai gane masa ba, musamman ma da Bahaushe ke cewa idan maciji ya sareka ka ga bakin tsumma sai gudu. Wannan ne kusan fargabar wasu a kasar Ghana sakamakon tsugunar da wasu Fursunonin Gwantanamo a kasar tasu.
Wasu na ganin wannan abu bai kamata ba saboda yanayin kasar na bukatar kayan aikin zamani don gane yakar ta'addanci. To sai gashi kwatsam kasar Amurka ta bukaci Ghana ta agaza ta tsugunar da wasu da ake zargi da ta'addanci ake tsare da su a gidan yarin Gwantanamo dake Cuba.
Wadannan mutane dai an dade tsare da su ba tare da tabbatar da wani laifi ko hukunci akan tuhumar da ake musu ba. To daga baya an so maida su kasarsu ta asali Yamal, amma saboda yanayin rikicin kasar da ake ciki sai aka fasa.
Inda kuma rahotanni suka nuna cewa wadannan mutane an basu zabi ne game da inda za a kaisu su zauna, sai suka zabi ghana. Wakilinmu Baba Yakubu Makeri ya aiko mana wannan rahoton daga Ghana.