‘Ya’yan KoKo dai shine sinadarin da ake yin alawar cakulan wato irin alawar nan mai maski da zaki da ake samu a manyan shagunan sayar da kayan kwalam da makulashe a duniya. Sannan KoKo din na kasar Ghana shi aka fi so a duniya don da shi ake yin wannan alawa mafi lagwada.
To sai dai kash, noman na KoKo a kasar yana shiga halin ni ‘yasu sakamakon wasu irin kwari da ke addabar itatuwansa. Haka kuma wani masanin harkar noma ya bayyana cewa ana bukatar wayar da kan manoman wannan dan itace.
Sannan kuma ana bukatar gwamnati ta ci gaba da tallafawa ta hanyar wayar da kan al’umma a kan muhimmancin wannan noma na abinda ke haifar da kudaden shiga a kasar. Bugu da kari kuma duk da kasar na samar da dan itacen da ake Cakulan da shi, to amma ‘yan kasar ba wani shan alewar.
Wannan ne yasa kasar ta ware ranar 14 ga watan Fabrairun kowace shekara a matsayin ranar tandar alewar mai maski da zaki. Kasancewar ranar 14 ga watan shine ranar da duniya take bukin ranar masoya ta balantayin a garuruwa musamman Turai.
Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahaman ya sha alwashin cewa za su inganta wannan sana’ar ta noman KoKo don ci gaba da samar da isashshen dan itacen da kuma inganta tattalin arzikin kasar tunda ana bukatarsa ba kadan ba a duniya. Wakilinmu Baba Yakubu Makeri ya hada mana rahoton musamman.