Wani Turmutsitsi Ya Hallaka Mutane 121 A Indiya

India

Matsanancin cunkoso da rashin mafita ne ya haifar da wani turmutsitsi a wani bikin addini a arewacin Indiya da ya hallaka mutane da dama, in ji hukumomi a ranar Laraba.

India

Turmutsitsin dai ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 121 yayin da masu aminci suka yi kusa da mai wa'azin don kokarin taba shi kuma hargitsi ya biyo baya.

Biyar daga cikin wadanda suka mutu a safiyar Laraba, in ji wani jami'in yankin Manish Chaudhry, kuma mutane 28 na ci gaba da jinya a asibiti.

India

Mummunan turmutsutsu na zama ruwan dare a bukukuwan addinin Indiya, inda ɗimbin jama'a ke taruwa a ƙananan yankuna masu ƙarancin ababen more rayuwa da ƙarancin matakan tsaro.

Kimanin mutane dubu 250 ne suka hallarci ta taron a ranar Talata wanda aka ba da izinin daukar nauyin 80,000 kawai. Ba a bayyana ko nawa ne ba suka samu shiga cikin tantin da aka kafa a akan wani fili mai laka a wani kauye a gundumar Hathras a jihar Uttar Pradesh ba.

Har ila yau, ba a bayyana abin da ya haifar da firgicin ba.

India

Amma babban ministan jihar, Yogi Adityanath, ya shaida wa manema labarai cewa jama'a sun ruga zuwa wajen mai wa'azin domin su taba shi a lokacin da yake saukowa daga dandalin

Wani rahoto na farko da ‘yan sandan suka fitar ya nunar da cewa dubban mutane ne suka yi dafifi a hanyar, kuma da yawa sun zame a kasa mai cike da laka, lamarin da ya sa suka fado suka murkushe a cikin jama’a.

Yawancin wadanda suka mutu dai mata ne.

-AP