Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

India Ta Kusa Wuce China A Yawan Jama’a


Jama'ar Indiya
Jama'ar Indiya

India, wacce ta gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2011, ba ta ce uffan ba kan wannan hasashe da Majalisar Dinkin Duniya ta yi.

Majalisar Dinkin Duniya ta fada a ranar Litinin cewa India za ta wuce Sin a matsayin kasa mafi yawan al’umma a karshen wannan watan.

Hukumar tattalin arziki da zamantakewa ta Majalisar Dinkin Duniya (DESA) ta ce, ya zuwa karshen watan Afrilu, ana sa ran yawan al’ummar India zai kai biliyan 1.425, wanda ke nufin za ta yi daidai, sannan za ta zarce yawan al’ummar Sin.

“Kasar Sin ta kai kokoluwar yawan al’umma da ya kai biliyan 1.426 a shekarar 2022 kuma ya fara raguwa. Hasashen ya nuna cewa yawan al’ummar kasar Sin na iya raguwa kasa da biliyan 1 kafin karshen karni,” in ji hukumar.

Sanarwar ta Hukumar DESa ta zo ne bayan Asusun Yawan Jama’a Na Majalisar Dinkin Duniya ya fada makon da ya wuce cewa Indiya za ta sami Karin mutane miliyan 2.9 fiye da China nan da zuwa tsakiya 2023.

Sanarwar ta haifar da tambayoyi game da ko India za ta iya maimaita abin al’ajabi na tattalin arziki da ya fitar da Sin daga kangin talauci da kuma shigar cikin manyan kasshen duniya

India tana tallata kanta a matsayin mai tasowa a duniya yayin da za ta karbi bakuncin taron kungiyar G-20, wanda zai gudana a New Delhi a watan Satumba. Kungiyar G-20 ta kunshi manyan kasashen masu karfin tattalin arziki a duniya.

Kwararru kan Matsugunan Jama’a sun ce rashin wadattatun bayanai ya sa bai yiwuwa a iya samu takamanman lokacin da India za ta iya zarce Sin a yawan jama’a. Ta yuwu ma har ma sun zarce din.

John Wilmoth, darektan sashen yawn jama’a na Majalisar Dinikin Duniya, a wani taron manema labarai a Majalisar Dinkin Duniya ya ce “Ba’a san takamanman lokaci wannan zarcewar ba, kuma ba za’a taba saninsa ba.”

India, wacce ta gudanar da kidayar jama’a ta karshe a shekarar 2011, ba ta ce uffan ba kan kiyasin Majalisar Dinkin Duniya.

Da alama lokacin da Indiya ta zarce China a yawan jama’a ta yuwu a janye shi idan Indiya ta gudanar da kidayar jama’a ta gaba.

Tsofaffin Jama'ar Indiya
Tsofaffin Jama'ar Indiya

Yawan jam’ar Sin ya kai kokoluwa a shekarar 2022 kuma ya fara raguwa.

Adadin tsofaffon kasar na karuwa yayin da adadin haihuwarsu ke raguwa, daga jarirai 1.7 ga kowace mace a shekarar 2017 zuwa 1.2 a shekarar 2022, a cewa bayanan Majalisar Dinkin Duniya.

Sabanin haka, India ce ke da mafi yawan matasa a duniya, wanda suka fi yawan haihuwa a duniya kuma ana samun raguwar mace-macen jarirai. Masana ba sa ganin bukatar fadakarwa game da yawan jama’a saboda yawan haihuwa na kasar yana raguwa, daga haihuwa sama da biyar ga kowace mace a cikin shekarun 1960 zuwa biyu a cikin 2022.

Kamfanin dillanci labarai na Associated Press ya raiwaito cewa ana sa ran yawan al’ummar Indiya zai daina karuwa kuma zai daidaita a kusa da shekarar ta 2064.

XS
SM
MD
LG