Aisha Buhari Ta Kaddamar da Cibiyar Kula Da Masu Juna Biyu a Daura

Cibiyar Kula Da Mata Masu Juna Biyu Da Aisha Buhari Ta Kaddamar a Daura

Uwargidan shugaban Najeriya Aisha Buhari, ta kaddamar da wani katafaren ginin cibiyar kula da mata masu juna biyu a garin Daura a jihar Katsina. Wannan cibiyar da uwargidan shugaban kasar ta dauki dawainiyar ginata, zata taimakawa kiwon lafiyar mata a yankin.

Cibiyar ta samu na’urorin da kayan aiki na zamani na gwaje-gwaje da na haifuwa kuma zata magance matsalolin da mata masu juna biyu ke fuskanta. Uwargidan shugaban ta ce tana fatan ire-iren wannan cibiya zasu mamaye Arewacin Najeriya ganin cewa nan ne mata masu juna suka yawan mutuwa.

Aisha Buhari tace wannan wani yunkuri ne na samar da kayan aiki na kiwon lafiyar mata da kuma gyara wdanda suka lalace. A don haka ta yi kira ga gwamnonin Najeriya da su taimakawa matarsu wurin farfado da kiwon lafiyar mata a jihohinsu.

Uwargidan shugaban kasa ta kuma kaddamar da wani shiri na tallafawa mata marasa karfi a jihar Katsina domin basu sana’o’I kuma su rage dogaro a kan gwamnati. Wadanda suka yi nasarar cin gajiyar wannan shiri sun samu kekunan dinki, da injinan nika da na yin taliya da sauransu.

Your browser doesn’t support HTML5

AISHA BUHARI