Idan dai ba a manta ba, tun bayan rikicin ‘yan shi’ar ne da sojojin Najeriya a Zaria aka cafke shugaban nasu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky bayan rasa rayukan mabiyan Malamin da dama ciki har da ‘ya’yansa da aka zargi sojojin da kashe su.
A watannin baya wata kotu a Najeriya ta bada umarnin sakin Shehin Malamin tare da gina masa sabon gida a inda yake so sakamakon rushe masa muhallin da aka yi.
Bugu da kari kuma a bashi diyyar Miliyoyin Nairori sakamakon cin zarafin da aka masa. To amma duk da wannan hukuncin na kotun, sakin El-Zakzaky ya ci tura. Wanda hakan ce ta sa mabiyan nasa ke ta zanga-zangar lumana don ganin an sake shi.
Ko a wannan ranar ma, mabiyan na El-Zakzaky sun bayyana cewa za su ci gaba da zanga-zangar lumana har sai an ji kukansu bisa dokar sakin Malamin nasu da aka zartar amma jami’an gwamnati da alhakin sakin nasa ya rataya a kansu suka yi burus da lamari.
Wakilinmu Hassan Maina Kaina ya halarci waje zanga-zangar a cikin rahon nan da ya aiko mana cikin murya.
Facebook Forum